in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Somaliya ta hallaka 'yan ta'adda 81 a wani harin soji ta sama a kudancin kasar
2017-11-12 13:12:08 cri
Gwamnatin Somaliya ta sanar da cewa, a kalla mayakan 'yan tada kayar baya 81 ta kashe a wani samame biyu da jami'an tsaro suka kaddamar a Jilib, dake tsakiyar kudancin Somaliya.

Ministan yada labaran kasar Abdurahman Omar Osman, ya bayyana cewa, an kaddamar da samamen ne da sanyin safiyar ranar Asabar, wanda dakarun Somaliya tare da tallafin dakarun kasa da kasa suka kaddamar, inda aka kaddamar da harin kan wani gida da suke kera makamai da kuma sansanin horaswa na mayakan 'yan ta'addan dake yankin Gedo.

Osman ya bayyana cikin wata sanarwa a Mogadishu cewa, dakarun tsaron Somaliya sun kaddamar da sintiri na musamman a yankin Jilib inda suka lalata sansanin kungiyar 'yan ta'adda na Al-Shabaab, da wajen da suke taruwa inda suke shirya kaddamar da hare-hare a yankin na Gedo. Ya ce an hallaka mayakan 81, kana an kwace wasu motoci da kuma lalata wasu manyan makamai.

Daga bisani ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, jami'an tsaron sun lalata wasu kayayyaki da 'yan ta'addan ke amfani da su wajen hada boma bomai wadanda suka hada da sinadarin TNT, RDX, potassium da kuma sinadarin sodium nitrate.

Hare-hare na baya bayan nan ya zo ne wasu 'yan sa'o'i bayan da dakarun Somaliya da na Amurka suka kaddamar da hare-hare ta sama a yankin Lower Shabelle da yammacin ranar Jumma'a. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China