in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Uganda za ta fara janye dakarunta daga Somalia
2017-11-09 10:16:48 cri
Rundunar sojin kasar Uganda ta sanar da cewa za ta fara janye dakarunta na kiyaye zaman lafiya da ta tura kasar Somalia a karshen watan gobe wadanda suke aiki karkashin kungiyar tarayyar Afrika AU da kwamitin tsaron MDD.

Mai magana da yawun rundunar sojin kasar birgediya Richard Karemire, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an dauki wannan mataki ne sakamakon shirin da aka tsara na janye dakarun sama da dubu 6, wadanda ke aiki a rundunar kiyaye zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afrika (AMISOM) zuwa ranar 31 ga watan Disamba.

AMISOM ta kunshi sojoji daga kasashen Uganda, Burundi, Kenya, Habasha da Djibouti wadanda aka tura su shiyyoyi 6 da suka hada da kudanci da tsakiyar Somalia.

Wakili na musamman na kungiyar tarayyar Afrika a Somalia Francisco Madeira, ya sanar da cewa za'a janye dakaru 1,000 daga cikin tawagar sojojin kiyaye zaman lafiyar 22,000 za'a janye su daga Somalia nan da ranar 31 ga watan Disamba. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China