in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IGAD ta bukaci daukar matakan warware rikicin dake addabar wasu yankunan Somalia
2017-11-15 10:17:12 cri
Kungiyar shugabannin kasashen Gabashin Afirka ta IGAD, ta yi kira ga sassan kasashen duniya, da su hada gwiwa wajen kawo karshen tashe tashen hankula dake addabar jihohin Puntland da Galmudug na Somalia.

Wata sanarwa da jagororin kungiyar suka fitar bayan kammala taron su na yini biyu, ta bayyana kudurin kungiyar na daukar dukkanin matakan da suka dace, ciki hadda hada kai da gwamnatin tarayyar kasar, da kuma mahukuntan jihohin biyu, wajen shawo kan rashin fahimtar juna da a baya ya haifar da barkewar rikici.

Jihohin biyu dai na rigima da juna game da ikon mallakar garin Galkayo. Yanzu haka Galmudug ce ke iko da kudancin garin, yayin da Puntland ke rike da arewacinsa.

A watan Janairu ne dai aka sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta, tsakanin shugaban jihar Puntland Abdiweli Mohammed Ali, da shugaban tsagin Galmudug Abdikarim Hussein, matakin da ya kawo karshen dauki ba dadin da ya barke tsakanin sassan biyu a watan Oktobar 2016, wanda ya sabbaba kisan mutane sama da 50, ciki hadda fararen hula, baya ga wasu mutanen 90,000 da suka rasa matsugunansu.

Yarjejeniyar dai ta haifar da kwarin gwiwar martaba juna tsakanin sassan biyu, tare da kawo karshen fadace fadace tsakanin dakarunsu. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China