Guterres wanda ya yi wannan tsokaci ne, yayin taron muharawa na ministocin kwamitin tsaron, ya ce ya dace kwamitin tsaron ya yi managarcin zabi a matakan da yake dauka, duba da irin kalubale da ke fuskantar kungiyar kasashe 5 na yankin sahel a fannin tsaro.
Kasashen dai sun hada da Mali, da Nijar, da Burkina Faso, da Chadi da Mauritania, wadanda tuni suka kafa wani shiri na fuskantar matsalar yawaitar bullar kungiyoyi na masu ikirarin jihadi, wanda ke yiwa yankin barazana.
Babban magatakardar MDDr ya ce idan ba a dauki matakai da suka dace ba, sauye sauye da ake fuskanta yanzu haka, na iya haifar da tashe tashen hankula masu tsanani a yankin, da ma sauran sassan masu makwaftaka.
Mr. Guterres ya kara da cewa, tallafawa kungiyar kasashen na G5, zai kasance bangare na hadin gwiwa da zai karfafa kuzarin nahiyar Afirka a fannin tunkarar matsalar tsaro.(Saminu Alhassan)