in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sin ya bayyana manufofin kasar wajen neman ci gaba cikin sabon zamani
2017-11-11 13:28:12 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron kolin shugabannin masana'antu da kasuwanci na kungiyar hadin gwiwar tattalin arzikin kasashen yankin Asiya da Pasifik wato APEC, da aka yi a birnin Da Nang na kasar Vietnam Jiya Jumma'a da yamma.

Yayin taron, Xi Jinping ya yi jawabi mai taken "yin amfani da damar kwaskwarima ta fuskar tattalin arzikin a kasashen duniya, wajen neman ci gaban yankin Asiya da Pasifik baki daya".

Wannan shi ne karon farko da shugaba Xi ya yi jawabi ga wani taron kasa da kasa tun bayan kammala taron wakilan JKS karo na 19.

Cikin jawabinsa, shugaban ya bayyana manufofin kasar Sin wajen neman ci gaban yankin Asiya da Pasifik cikin hadin gwiwa a wani sabon zamani na gaba.

Wakiliyarmu Maryam Yang ta hada mana cikakken rahoto game da jawabin.

Cikin jawabinsa, shugaba Xi ya ce, zurfafa harkokin kwaskwarima wani sabon nauyi ne ga kasar Sin, yayin samar da kyawawan damammakin neman ci gaba. A shekarar 2018 mai zuwa, kasar Sin za ta yi murnar cika shekaru 40 da gudanar da manufofin yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga kasashen waje, inda za ta dauki karin matakai ta fuskar yin kwaskwarima a cikin gida, yayin bude kofa ga kasashen waje ta yadda zai dace da yanayin bunkasuwar kasa da kasa.

Haka kuma, za a inganta ayyukan dake shafar shirin "ziri daya da hanya daya", da kuma samar da manufofin da za su dace da yin cinikayya da zuba jari a tsakanin bangarori daban daban, ta yadda za a tallafawa al'ummomin kasashen da abin ya shafa, da kuma samar musu makoma mai kyau.

A sa'i daya kuma, za a ci gaba da kyautata zaman rayuwar jama'ar kasar Sin, domin cimma burin kawar da talauci a kasar baki daya zuwa shekarar 2020. Haka kuma, kasar Sin za ta tsaya tsayin daka wajen neman ci gaba cikin kwanciyar hankali, sannan za ta dukufa wajen gina sabuwar dangantaka a tsakanin kasa da kasa iri na mutunta juna, kiyaya adalci da kuma yin hadin gwiwa yadda ya kamata.

Kana, shugaba Xi ya kuma nuna damuwarsa kan matsalolin da ake fuskanta wajen neman bunkasar tattalin arzikin duniya, inda ya kuma ba da shawarwari guda hudu kan yadda kasashen Asiya da yankin Pasifik za su yi hadin gwiwa a tsakaninsu domin fuskantar kalubalen dake gabansu a wannan fanni.

Xi Jinping ya ce, ya kamata a ci gaba da yin hadin gwiwa a tsakanin bangarori daban daban a fannin raya tattalin arziki ta yadda za a cimma moriyar juna, da kuma sabunta tsarin wannan fanni domin kara karfin neman bunkasuwar tattalin arziki. Sa'an nan, a karfafa mu'amala domin taimakawa juna da kuma neman ci gaba tare. Har ila yau, ya ce ya kamata a ba da gudummawa ga al'ummomin kasa da kasa wajen cimma sakamakon bunkasuwar tattalin arziki.

Haka zalika, shugaba Xi ya jaddada cewa, ya kamata mabobin kungiyar APEC su hada hannu wajen gina tsarin tattalin arzikinta irin na bude kofa ga kasashen waje, ta yadda zai dace da samar da sauki wajen gudanar da harkokin cinikkaya da zuba jari. A sa'i daya kuma, ya kamata a yi kwaskwarima kan tsarin tattalin arziki, domin raya kasuwannin kasashen yankunan, yayin karfafa mu'amalar dake tsakanin bangarori daban daban domin ba da taimako ga bunkasuwar tattalin arziki yadda ya kamata.

Bugu da kari, shugaba Xi yana ganin cewa, ya kamata a shigar da ka'idojin yin ma'amala da hadin gwiwa cikin tsarin neman bunkasuwa, yayin dukufa wajen gina tsari mai cike da adalci da kuma karfi, ta yadda za a ba da gudummawa wajen kiyaye yanayin daidaiton zaman takewar al'umma baki daya.

Shugaba Xi ya kuma kara da cewa:

Ya ce, ya kamata al'ummomin yankin Asiya da Pasifik su yi hadin gwiwa wajen gina wata makoma mai zaman lafiya, mai zaman karko da kuma ci gaba. Haka kuma, dangantakar fahimtar juna da yin hadin gwiwa da aka gina a tsakanin mambobin kungiyar APEC za ta ba da tabbaci wajen gudanar da hadin gwiwarsu yadda ya kamata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China