Shugaba Xi ya ce a matsayin APEC na kungiyar kawancen tattalin arziki mafi girma a yankin Asia da Pasifik, ita kuma kungiyar ASEAN ta kawancen yanki mai dimbin damarmaki, hadin gwiwa tsakaninsu na da kyakkyawar makoma.
Shugaba Xi ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da shugabannin bangarorin biyu, ya na mai zayyana manufofi da tsare-tsare iri guda da kungiyoyin ke da su. (Fa'iza Mustapha)