in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi Jinping ya ce Sin za ta duba yiwuwar samar da tashoshin ruwa marasa shinge
2017-11-10 20:45:55 cri
A yau Juma'a ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana aniyar kasar sa, ta duba yiwuwar sanya wasu tashoshin ruwan kasar kasancewa karkashin tsarin cinikayya maras shinge.

Shugaba Xi Jinping wanda ya bayyana hakan cikin jawabin da ya gabatar, yayin bude taron jagororin APEC dake gudana a birnin Da Nang na kasar Vietnam, ya ce Sin na da burin kara fadada gyare gyare ga tsarin da take bi, game da gudanar da cinikayya cikin 'yanci a wuraren na gwaji.

A wani ci gaban kuma, shugaba Xi, ya alkawarta baiwa sassan harkokin cinikayya dama ta bai daya a cikin kasar Sin, a gabar da kasar ta sa ke kara bude kofofin ta ga sassan duniya.

Shugaba Xi ya kuma yi kira ga mambobin kungiyar APEC, da su kara daukar matakan bude tsarin tattalin arzikin su, ta yadda zai zama mai cike da daidaito, ya game dukkan sassan duniya, matakin da ya hakikance zai zamo mai alfanu ga dukkanin kasashen duniya, a dukkanin matakai na zamantakewar al'umma.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China