Shugabannin sun gana ne a wani bangare na taron shugabannin kungiyar hadin kan tattalin arzikin yankin Asia da Pasifik APEC dake gudana a birnin Da Nang na kasar Vietnam.
La'akari da ganawar da shugabannin biyu suka sha yi, shugaba Xi ya ce kokarinsu na ganin sun inganta huldar dake tsakanin Sin da Rasha cikin lokaci mai tsawo ya cimma dimbin nasarori.
Shugaba Putin ya kuma taya murnar nasarar kammala babban taron JKS na 19, inda ya lashi takobin Rasha za ta ba batun raya huldarta da kasar Sin muhimmanci.
Ya ce a shirye Rasha take ta inganta huldarta da kasar Sin kan harkokin yanki da na duniya, tare da kara tuntubar juna da nufin ganin an cimma yarjejeniyar cinikayya mara shinge tsakanin Asia da Pasifik. (Fa'iza Mustapha)