in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya tashi daga birnin Beijing domin halartar taron shugabannin kungiyar APEC da za a yi a Vietnam
2017-11-10 11:14:27 cri
Da safiyar yau Jumma'a ne, shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, Xi Jinping ya tashi daga birnin Beijing, domin halartar taro karo na 25, na shugabannin kungiyar hadin gwiwar tattalin arzikin kasashen yankin Asiya da Pasifik wato APEC, wanda za a yi a birnin Da Nang na kasar Vietnam.

Baya ga taron, shugaba Xi Jinping, zai gudanar da ziyarar aiki a kasashen Vietnam da Laos, bisa gayyatar da shugaban kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Vietnam Nguyen Phu Trong da shugaban jamhuriyar kasa ta Vietnam Tran Dai Quang da kuma shugaban kwamitin tsakiyar jam'iyyar dimokuradiyyar jama'a ta kasar Laos Boungnang Vorachith suka yi masa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China