in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya yi kira da a gaggauta aikin neman sulhu a Sudan ta Kudu
2017-05-25 13:00:10 cri
Zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Liu Jieyi, ya bayyana cewa, shimfida zaman lafiya da zaman karko a kasar Sudan ta Kudu shi ne burin bangarori daban daban na kasar Sudan ta Kudu, kuma hanyar siyasa ita ce hanya kadai da za a iya warware matsalar kasar, ta yadda za a iya samun cikakken zaman lafiya a kasar.

Mr. Liu ya bayyana haka ne a yayin taron tattaunawa kan batun Sudan ta Kudu na MDD da aka gudanar, inda ya kuma bayyana cewa, ana fuskantar kalubaloli da dama a kasar Sudan ta Kudu, ciki har da matsalolin tsaron siyasa, ci gaban tattalin arziki da kuma karancin abinci wanda al'ummomin kasar suke fama da shi, shi ya sa, ya kamata kasar Sudan ta Kudu da gamayyar kasa da kasa su dukufa tare da yin hadin gwiwa domin warware matsalolin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China