Ministan kiwon lafiya na Sudan ta Kudu Riek Gai Kok, da jakadan Sin dake Sudan ta Kudu He Xiangdong, sun bada lambar yabo ga tawagar likitoci na Sin.
Bayan da aka tura tawagar zuwa kasar Sudan ta Kudu a watan Satumba na shekarar bara, tawagar likitoci ta 7 ta Sin ta kammala dukkan ayyukan da tawagar musamman ta MDD dake Sudan ta Kudu ta bayar, kana ta bada jinya ga fararen hula 12 da suka ji rauni a sakamakon bala'u, da yara 8 dake sansanin 'yan gudun hijirar da suka kamu da cututtuka, da mutane 3 da suka kamu da cuta mai tsanani a sansanin bisa tunanin sada zumunta a tsakanin Sin da Afirka da yada zaman lafiya, kuma ta bada gudummawa wajen bada jinya ga mutanen da suka samu raunuka a sakamakon hadarin jirgin sama a kasar, da kuma bada jinya ga wata mata mai juna biyu saboda dakatar mata da zubar jini mai tsanani bayan da ta haihu. Yawan mutanen da tawagar ta bada jinya ya zarta 400, tare da taimakawa jarirai 6. (Zainab)