in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Al'ummar kasar Sudan ta Kudu sun bayyana rashin jin dadi game da kin gudanar da bikin zagayowar ranar 'yancin kai
2017-07-10 10:18:18 cri
Yayin da ake tsaka da rikicin da ya shafe shekaru 3, al'ummar kasar Sudan ta Kudu, sun bayyana rashin jin dadi game da yadda a karo na biyu, kasar ta gaza gudanar da bikin murnar ranar 'yancin kai, inda a bana ta ke cika shekaru 6 da smaun 'yanci a ranar 9 ga watan nan.

Gwamnatin Shugaban kasar Salva Kiir, ta ce ba ta samu damar gudanar da bikin ranar samun 'yancin kai na bana a birnin Juba ba, saboda matsalar tattalin arziki, la'akari da yadda rikici ya haifar da koma baya ga samar da man fetur wanda shi ne kashin bayan tattalin arzikin kasar.

Dau Akoi Jurkun Kwamshinan yankin Twic na tsakiya dake jihar Jonglei na arewacin kasar, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, duk da kalubalen da ake fuskanta, ya kamata kowa da kowa ya yi murnar nasarar samun 'yanci da kasar ta yi daga Sudan a shekarar 2011.

Ya kara da cewa, bai kamata rikicin siyasa da ke gudana sanadiyyar takkadama da ta kunno kai tsakanin shugaba Kiir da tsohon mataimakinsa karkashin gwamnatin hadin kan al'umma, ya raba kan jama'ar kasar ba, yana mai kira da a tabbtar da hadin kai tare da hawa teburin sulhu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China