Mai magana da yawun MDD Farhan Haq wanda ya bayyana hakan ga taron mane ma labarai, ya ce karancin kudin ya kuma tilastawa shirin na WFP dakatar da baiwa rabin mutanen da ya ke da niyar agazawa da kuma rabin abincin da ya yi niyar samarwa.
Yanzu haka, shirin na WFP yana bukatar dala miliyan 21.5 cikin gaggawa, domin ya samar da agajin ceton rai a kasar har zuwa watan Yuni.
Kakakin MDD ya kuma bayyana damuwa kan rahotanni da MDDr ke samu game da yadda kungiyoyi masu dauke da makamai a kasar ke tayar da tashin hankali da take hakkin bil-Adama.
Tun a watan Janairun shekarar 2016 ne tawagar MDD da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar (MINUSCA) ta gudanar da bincike game da zargin take hakkin bil-Adama da aka aikata a yankunan Koui da Bocaranga, kuma tuni ta kammala mika rahotanta.
Bayanai na nuna cewa, tawagar ta MINUSCA ta tabbatar da kisan fararen hula 13,da mata 7 da aka yiwa fyade, baya da rahotannin kisa da fyade da ake zargin an yiwa mutane sama da 100. (Ibrahim)