Babban magatakardan MDD Antonio Guterres ya yabawa kasar Sin game da goyon bayan da ta ke ba Majalisar da kuma ra'ayin nan na kasancewar bangarori da dama, yana mai cewa a matsayinta na mamba a kwamitin sulhu na Majalisar wadda ke da kujerar dindindin kuma babbar kasa mai tasowa, kasar Sin tana ba da gudumamwar a zo a gani cikin harkokin MDD da na kasa da kasa.
Antonio Guterres ya bayyana haka ne a jiya, lokacin da yake ganawa da zaunannen wakilin kasar Sin a MDD mai barin gado Liu Jieyi, inda ya ce, cikin shekaru 4 da suka gabata, Mr. Liu ya taka mihimmiyar rawa wajen inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da MDD, haka kuma, MDD tana son ci gaba da karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar domin kiyaye zaman lafiyar duniya, da kuma tallafawa al'ummomin kasa da kasa. (Maryam)