in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya jaddada bukatar hadin gwiwar bangarori daban daban don daidaita batun nukiliya a zirin Koriya
2017-09-14 11:09:44 cri
Jakada Shi Zhongjun, zaunannen wakilin kasar Sin a ofishin MDD dake birnin Vienna na kasar Austria, ya halarci taron majalisar hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa a jiya Laraba, inda ya yi tsokaci kan gwajin makamin nukiliya da Koriya ta Arewa ta yi.

A cewar wakilin kasar Sin, Koriya ta Arewa ta yi biris da shawarar da gwamyyar kasa da kasa, ciki har da kasar Sin, suka ba ta, ta dakatar da gwajin makaman nukiliya. Maimakon daukar shawarar, sai kasar ta sake yin gwajin nukiliya a ranar 3 ga wata, lamarin da ya haifar da illa ga tsarin hana bazuwar makaman nukiliya a duniya, da sabawa kudurin kwamitin sulhu na MDD, da ra'ayin bai daya na gamayyar kasa da kasa. Matakin da Koriya ta Arewa ta dauka ya tsananta yanayin rikici a zirin Koriya, da raunata kwanciyar hankali da zaman lafiya a yankin. Saboda haka kasar Sin ta riga ta bayyana ra'ayinta na rashin amincewa da matakin.

Wakilin kasar Sin ya kara da cewa, kasarsa ta kalubalanci Koriya ta Arewa, da ta martaba niyyar gamayyar kasa da kasa ta kawar da makaman nikiliya daga zirin Koriya, da biyayya ga kudurin kwamitin sulhu na MDD, tare da magance daukar makakin da zai iya tsananta yanayin da ake ciki, wanda zai haifar da illa ga ita kanta, sa'an nan ta koma teburin shawarwari don neman daidaita al'amarin. Har ila yau, ya ce kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan kokarin kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya, da kare tsarin hana yaduwar makaman, da kokarin kare zaman lafiya a yankin arewa maso gabashin nahiyar Asiya. Don neman cimma wadannan buri, kasar Sin tana ta kokarin yin sulhu tsakanin bangrorin da batun ya shafa, duk da cewa ba ta da alakar kai tsaye da maganar nukiliya a Koriya ta Arewa.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China