Mukaddashin shugaban zaunanniyar tawagar kasar Sin da ke MDD Wu Haitao ya bayyana jiya Alhamis, cewar kasashen dake aika sojoji da 'yan sanda su ne kashin bayan aikin wanzar da zaman lafiya na MDD, ya kamata a mayar da hanlali kan rawar da irin wadannan kasashe ke takawa
Wu ya kara da cewa, a cikin shekaru biyu da suka gabata, kasar Sin ta horar da masu wanzar da zaman lafiya fiye da 800 don MDD da kasashen da abin ya shafa, kuma ta aika da rukunin farko na jiragen sama masu saukar ungulu don taimaka wa MDD wajen gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya a Afirka. Ban da wannan, kasar Sin na kokarin aiwatar da shirin samar wa kungiyar tarayyar Afirka AU taimako ta fuskar aikin soja da darajarsa ta kai dala miliyan 100, baya ga taimakawa kasashen dake tura sojoji musamman ma kasashen Afirka wajen kara karfinsu na samar da zaman lafiya, yayin da kasar Sin da MDD ke kokarin samar da asusun wanzar da zaman lafiya.(Kande Gao)