in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya bayyana ra'ayin kasarsa kan batutuwan tsaron zirga-zirgar jiragen sama da yaki da ta'addanci
2017-09-28 16:05:09 cri
A jiya Laraba ne, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Wu Haitao ya bayyana ra'ayin kasar kan harkokin kiyaye tsaron jiragen sama da kuma yaki da ta'addanci.

Mr. Wu ya ce, ya kamata kasashen duniya su tsaya tsayin daka kan yaki da duk wani nau'in ta'addanci daga dukkan fannoni, kana ya dace gamayyar kasa da kasa su taimakawa kasashe masu tasowa wajen warware matsalolin dake shafar tsaron zirga-zirgar jigaren sama musamman ma a fannonin inganta binciken da ake yi a filin jiragen sama, karfafa matakan tsaro yadda ya kamata da kuma yin rigakafin aukuwar matsalolin da abin ya shafa da dai sauransu, ta yadda za a ba da gudummawa wajen kyautata kwarewar kasashe masu tasowa a fannin kiyaye tsaron zirga-zirgar jiragen sama. Haka kuma, ya kamata a taimakawa kasashe a fannonin da suke bukata, tare da girmama 'yancin kasashen.

Bugu da kari, ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da inganta aikin yaki da ta'addanci a fannin zirga-zirgar jiragen saman fasinja, da dukufa wajen kyautata ayyukan kasashen da abin ya shafa. Kana, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa da kungiyar zirga-zirgar jiragen sama ta kasa da kasa wato ICAO, a fannonin kiyaye tsaron zirga-zirgar jiragen sama da kuma gudanar da ayyukan sa ido kan yanayin tsaro da dai sauransu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China