Haka kuma, kafofin watsa labaran wuraren sun ruwaito kalaman babban kwamandan sojojin gwamnatin kasar Abdulahi Ali Anod yana cewa, a halin yanzu, sojojin gwamnatin sun riga sun karbe ikon wurare da dama a jihohin biyu, wadanda suka taba zama karkashin ikon kungiyar Al-Shabaab. Sa'an nan, za su ci gaba da daukar matakan soja kan dakarun na kungiyar Al-Shabaab. (Maryam)