in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD za ta taimakawa matasan Somalia wajen zuba jari a kamfanin madara
2017-10-11 11:11:40 cri
MDD ta yi alkawari tallafawa matasa 'yan kasar Somalia wajen samar musu da fasahohin zamani wadansa za su taimake su wajen habaka ci gaban kamfanin samar da madara a kasar.

Da yake jawabi a taron kwanaki 7 da aka gudanar a Mogadishu, game da yadda za'a inganta fasahohi, mataimakin wakilin musamman na sakatare janar na MDD dake Somalia, Peter de Clercq, ya zaburar da matasan kasar inda ya bukace su da su zakulo wasu hanyoyi da kuma shawarwarin da za'a yi amfani da su wajen magance matsalolin tattalin arziki dake damun kasar.

Cikin wata sanarwa da ofishin MDD dake kasar Somalia (UNSOM) ya fitar, De Clercq, ya bayyana gamsuwarsa da irin shawarwarin da aka gabatar, yana mai cewa hakan alamu ne dake nuna cewa za'a iya yin amfani da shawarwarin da suka shafi fasahohin wajen magance matsalolin cikin gida a kasar.

Ya ce za su duba irin matakan da za su bi wajen taimakawa matasan ta hanyar aiwatar da muhimman shawarwarin da aka gabatar don yin amfani da su wajen ciyar da tattalin arzikin kasar gaba, kana ya yi alkawarin cewar MDDr za ta ci gaba da ba su goyon baya.

Shawarar wadda ita ce irinta ta farko da ta samu goyon bayan MDD don ciyar da fasahohi gaba a Somaliya, taron da aka gudanar ya samu halartar matasa maza da mata 40 'yan kasar Somalia, inda suka yi baje kolin muhimman shawarwarin da za'a yi amfani da su wajen inganta kamfanin madara na kasar. Kana mahalarta taron sun samu tallafi da goyon bayan shirin raya ci gaban kasashe na MDD, UNDP wanda ya taimaka musu game da yadda za su inganta harkokin kasuwancinsu. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China