in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Amurka sun yi luguden wuta kan mayakan IS a Somaliya
2017-11-04 12:13:07 cri
Sojojin Amurka sun ce sun yi luguden wuta har sau biyu kan mayakan kungiyar IS dake Somaliya, lamarin da ya hallaka mayakan kungiyar da dama.

Wata sanarwa da rundunar sojan Amurka dake aiki a Afirka ta fitar jiya, ta ce sojojin Amurka sun kai farmaki ta sama kan dakarun IS dake arewa maso gabashin kasar Somaliya.

Sanarwar ta kara da cewa, har yanzu sojojin na nazarin sakamakon farmakin. Kuma za su ci gaba da kokarin yaki da ayyukan ta'addanci tare da rundunar sojan Tarayyar Afirka gami da dakarun gwamnatin kasar Somaliya. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China