in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 6 sun mutu wasu 8 sun samu raunuka a Mogadishu
2017-10-29 12:34:26 cri
A kalla mutane 6 ne aka hallaka kana wasu mutane 8 suka samu raunuka a wani harin da aka kaddamar a wata mota a wajen wani shahararren otel mai suna Nasahablod 2 a birnin Mogadishu a ranar Asabar.

Wani jami'in dan sanda wanda ya bukaci a sakaye sunansa, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, akwai mutane masu yawa da harin ya rutsa da su a inda lamarin ya faru. Ya ce bam na biyu ya sake tashi ne jim kadan bayan tashin na farkon duka a wuri guda.

Mazauna wajen sun bayyana cewa hayaki ya yi matukar turnukewa bayan fashewar boma boman inda kuma daga bisani aka ji karar harbe-harbe a wajen otel din.

Mazauna wajen sun ce, jami'an ba da agajin gaggawa sun kwashe mutane masu yawa da suka samu raunuka bayan da dan kunar bakin waken ya tada boma bomai a cikin wata mota a wajen otel din.

Wani da ya ganewa idonsa faruwar lamarin ya ce, bam na biyu ya tashi ne a daidai lokacin da wata babbar mota ke kokarin haurawa kan wasu kananan motoci a daidai lokacin da jami'an aikin ceto ke kokarin kutsawa inda lamarin ya auku. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China