Mai Magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Kasar Sin Lu Kang wanda ya bayyana hakan yau yayin taron manema labarai, ya ce kasar Sin tana mika sakon ta na ta'aziyya ga iyalan wadanda suka mutu tare da jajantawa wadanda suka jikkata sanadiyyar wannan hari.
Ya ce kasar Sin tana nuna rashin amincewa da duk wani nau'i na ta'addanci, kana tana goyon bayan matakan da gwamnatin Somaliya take dauka na yaki da ayyukan ta'addanci da tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar.
Lu Kang ya ce a shirye kasar Sin ta ke ta hada kai da kasashen Afirka ciki har da kasar Somaliya domin tunkarar kalubalolin da ayyukan ta'adannci suka haddasa, tare da taka muhimmiyar rawa a kokarin da ake na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afirka.
Rahotanni na cewa, harin na ranar Asabar da aka kaddamar a kusa da yankin cinikayya ta hanyar amfani da wata babbar mota shake da abubuwan fashewa, ta tarwawatse ne a kusa da mashigin otel din Safari, lamarin da ya lalata wurin baki daya.
Shugaba Mohamed Abdullhi Mohamed na Somaliya dai ya ayyana zaman makoki na kwanaki uku a fadin kasar.(Ibrahim)