Mataimakin kwamishinan 'yan sandan shirin AMISOM, Christine Alalo, ya bayyana cewa, sabbin jami'an 'yan sandan da aka baiwa horon, za su horas da jami'an 'yan sandan kasar Somalia ne game da kyawawan dabarun wanzar da tsaro.
A wata sanarwa da aka fitar a Mogadishu, Alalo, ya bayyana cewa, manufar shirin bada horon shi ne domin baiwa jami'an 'yan sandan na AU damar samun kwarewar gudanar da aiki kasancewar sun fara gudanar da aikinsu na wanzar da zaman lafiya na tsawon shekara guda a Somalia.
Kasashen Najeriya da Saliyo suna daga cikin kasashe 6 dake bada tallafin jami'an 'yan sandan wanzar da zaman lafiya a Somalia, sauran su ne kasashen Kenya, Ghana, Uganda da Zambiya. (Ahmad Fagam)