in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin gwamnatin Siriya sun karbe ikon birnin Deir ez-Zor baki daya
2017-11-03 20:12:31 cri
Rundunar sojan gwamnatin kasar Syria ta bayyana cewa, dakarunta sun yi nasarar kwace birnin Deir ez-Zor kana babban birnin lardin dake gabashin kasar baki daya. Wannan wata babbar nasara ce a yakin da sojojin ke yi da kungiyar IS.

Haka kuma, sojojin gwamnatin sun kashe dakarun kungiyar IS da dama, baya ga makamai da kuma harsashinsu masu yawa da suka kwace daga hannun mayakan. A halin yanzu sojojin suna bincike don gano nakiyoyin da dakarun kungiyar IS suka binne a titunan birnin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China