in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin gwamnatin Siriya sun karbe ikon wani muhimmin yanki dake jihar Deir ez-Zor
2017-11-03 11:02:05 cri
Sojojin gwamnatin Siriya sun bayyana a jiya Alhamis cewa, sun yi galaba kan wasu mayakan kungiyar nan ta IS, lamarin da ya ba su damar karbe ikon wani muhimmin yanki dake jihar Deir ez-Zor na gabashin kasar.

Wata majiya daga bangaren sojojin Siriya ta ce, sojojin sun karbe ikon yankin Hamidiyeh na birnin Deir ez-Zor, inda suka hallaka mayakan IS da dama, tare kuma da lalata motocin sulke da motoci masu dauke da boma-bomai da dama. Rahotanni sun ce, akwai cibiyoyin mayakan kungiyar IS da dama a wannan yanki na Hamidiyeh, don haka, karbe ikonsa da sojojin gwamnatin Siriya suka yi, muhimmiyar nasara ce.

Har wa yau, majiyar ta ce, har yanzu ana samun wasu wuraren dake karkashin ikon mayakan IS a birnin Deir ez-Zor, kana, ta musunta ikirarin dake cewa, sojojin gwamnati sun riga sun karbe ikon birnin gaba daya.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China