Wani jami'in gwamnatin kasar ya bayyana cewa, wannan shi ne babban ci gaba da aka samu a matakan soja da aka dauka a kan kungiyar IS, lamarin da zai kawo karshen kungiyar IS a lardin Deir al-Zour baki daya.
Rundunar sojan kasar Syria ta bayyana cewa, halin yanzu, sojojin gwamnatin kasar suna ci gaba da kai hare-hare kan kungiyar IS dake birnin Deir al-Zour ta hanyoyi guda biyu.
Lardin Deir al-Zour yana gabashin kasar Syria, muhimmin wurin da ake hako man fetur kasar Syria, kana ya yi iyaka da kasar Iraki. Tun a shekarar 2014 ne dai kungiyar IS ta ke rike da lardin. (Maryam)