Babbar hedkwatar ba da shawara ga sojojin kasar Turkiya ta sanar a jiya Litinin cewa, sojojin kasar sun shiga cikin kasar Syria a ranar 8 ga wata don gudanar da aikin bincike da sa ido.
Sanarwar da Hedkwatar ta fitar ta ce, 'yan kundumbala na sojojin Turkiya za su kafa tasoshin bincike a cikin Syria, domin sa kaimi ga aiwatar da sakamakon da aka samu cikin shawarwarin Astana, wato kafa yankin tuddan tsira a kasar.
A cikin shawarwari da aka yi kan batun Syria a birnin Astana na kasar Kazakhstan daga ranar 14 zuwa ranar 15 ga watan jiya, kasashen Rasha da Turkiya da Iran, sun cimma daidaito kan cewa, za a kafa yankuna hudu na sassauta rikici a kasar Syria. Sannan kasashen uku za su tura masu sa ido zuwa yankunan bisa umurnin hadaddiyar kungiyar aiki ta kasashen. (Kande Gao)