in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin gwamnatin Syria sun sanar da kame birnin Mayadeen
2017-10-15 14:04:28 cri
Jiya Asabar, bangaren sojojin gwamnatin Syria ya sanar da cewa, ya kame birnin Mayadeen, muhimmin birni na lardin Deir ez-Zor dake gabashin kasar daga hannun kungiya mai tsattsauran ra'ayi ta IS.

Bangaren sojojin Syria ya kara da cewa, a karkashin goyon bayan kawancensa, sojojin gwamnatin sun yi yaki mai tsanani tare da IS, har sun kashe dakarun kungiyar da dama.

A wannan rana kuma, rundunar Syrian Democratic Forces wato SDF a takaice, ta bayar da sanarwa cewa, za ta mamaye Ar Raqqah, wato sansanin kungiyar IS dake kasar ta Syria a cikin 'yan kwanaki masu zuwa. An ce, dakarun kungiyar IS kimanin 100 sun riga sun mika wuya a ranar 13 ga wata a Ar Raqqah, amma duk da haka ana fama da yaki a wurin.

A wani labari na daban da aka bayar an ce, a ranar 14 ga wata, ma'aikatar harkokin wajen kasar Syria ta bukaci sojojin kasar Turkiya da su janye jiki ba tare da gindaya sharadi ba daga lardin Idlib dake arewa maso yammacin kasar ta Syria. Kamfanin dillancin labarun Syria ya ruwaito labarin ma'aikatar harkokin wajen kasar na cewa, bangaren Syria ya yi zargi kan shiga lardin Idlib da sojojin Turkiya suka yi ba tare da samun izni ba, yana ganin cewa, wannan ya keta ikon mallakar cikakkun yankunan kasar Syria, kana ya saba wa dokokin kasa da kasa. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China