Shugaban kawancen 'yan hamayya na kasar Kenya wato NASA Raila Amolo Odinga ya bayyana wa kafofin yada labaru jiya Talata cewa, bai amince da sakamakon zaben shugaban kasar da aka sake gudanarwa a ranar 26 ga watan jiya ba.
A cewar Odinga, zaben na ranar 26 ga watan jiya, ya saba kundin tsarin mulkin kasar. Yana mai cewa, kamata ya yi a gaggauta gudanar da babban zabe kamar yadda kundin tsarin mulki da dokoki suka tanada, kamar yadda kotun kolin kasar ta bukata. (Tasallah Yuan)