in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta mutunta zaben da jama'ar Kenya suka yi
2017-10-31 18:56:32 cri

Kasar Sin ta bayyana cewa, tana mutunta zaben da jama'ar Kenya suka yi. Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madan Hua Chunying wadda ta bayyana hakan yau Talata a nan birnin Beijing, bayan da hukumar zaben kasar Kenya ta sanar da shugaban Kenya Uhuru Kenyatta a matsayin wanda ya sake lashe zaben da aka sake shiryawa a kasar, ta ce kasar Sin na fatan sassa daban daban na Kenya za su kasance masu kishin kasa da jama'arsu fiye da komai, kana su kai zuciya nesa tare da nuna ya kamata wajen daidaita duk wani sabani ta hanyar da ta dace, a kokarin tabbatar da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar ta Kenya. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China