Bayan da aka gabatar da sakamakon zaben, Kenyatta ya yi jawabi, inda ya nuna godiya ga masu jefa kuri'un a wannan karo, kana ya yi kira ga jama'a da su kiyaye zaman lafiya da tabbatar da hadin kai.
Bisa kididdigar da hukumar zaben kasar ta fitar, mutane miliyan 7 da dubu 600, cikin jimillar masu jefa kuri'u a zaben, wanda ya kunshi fiye da mutum miliyan 19 da dubu 600 da suka yi rajista ne suka jefa kuri'un su.
Ko da yake an gudanar da zaben a yawancin yankunan kasar, amma a sakamakon barazanar tsaro, ba a kada kuri'u a yankuna 25 ba a ranar 26 ga watan, wato adadin da ya kai kashi 8.6 cikin dari na adadin yankunan da suka yi zaben a karon farko.
Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Kenya suka bayar a wannan rana cewa, kawancen 'yan adawa na NASA, ya ki amincewa da sakamakon zaben da aka yi a ranar 26 ga wannan wata. (Zainab)