Hukumar zaben kasar Kenya, ta ce ta dage gudanar da zabe a wasu yankunan yammacin kasar 4 da ake zanga-zanga zuwa ranar Asabar.
Hukumar ta ce ta dakatar da zabe a yankunan Homa da Siaya da Migori da kuma Kisumu, inda 'yan adawa suka fi yawa, saboda tsaikon da zanga zanga da barazana kan jami'an zabe suka haifar.
Zanga-zangar adawa da zaben ya barke ne a yammacin kasar da ya kasance matattarar 'yan adawa da kuma yankin Kibera na Nairobi, a daidai lokacin da aka fara gudanar da sabon zaben shugaban kasar a jiya Alhamis.
Rikici ya barke tsakanin masu zanga-zanga da 'yan sanda, inda suka yi musayar wuta a yankunan, a lokacin da 'yan sanda ke sintiri yayin da aka fara zaben. (Fa'iza Mustapha)