in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IGAD EOM ta yi na'am da sakamakon zaben Kenya da aka sake
2017-11-01 11:07:41 cri
Tawagar sanya ido a zaben kasar Kenya da aka maimaita karkashin inuwar kungiyar ci gaban yankin gabashin Afirka ko IGAD EOM, ta yi na'am da sakamakon zaben na ranar 26 ga watan Oktoba, tana mai kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki a siyasar kasar da su warware takaddamar dake tsakanin su domin ci gaban kasar.

Wata sanarwa da tawagar ta fitar a birnin Nairobi, ta ce a runfunan zabe 79 da ta halarta, an kada kuri'u cikin lumana ba tare da wata matsala ba. Kuma an bude da yawa daga rumfunan zaben a kan lokaci bisa tsari. Sanarwar ta ce bisa abun da jami'an sa idon suka gani, kayan aiki sun isa runfunan kada kuri'u cikin nasara.

Tawagar mai kunshe da jami'ai 21, wadanda suka gana da masu ruwa da tsaki a shirya zaben, sun jinjinawa shirin da mahukuntan kasar ta Kenya suka yi game da tabbatar gudanar zaben cikin nasara.

Kaza lika tawagar jami'an ta nuna gamsuwa, bisa amfani da aka yi da na'urorin tantace masu zabe na zamani, da tsaro da aka samar don ganin maimaicin babban zaben kasar ya gudana cikin nasara. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China