An yi rajistar masu zabe kusan miliyan 20 a duk fadin kasar. Da misalin karfe shida, agogon kasar, aka fara zaben, kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar ta ce, ana sa ran za a kawo karshen kada kuri'ar da misalin karfe biyar na yammacin ranar. Amma za a tsawaita lokacin a wasu rumfunan zabe da ba a bude su kan lokaci ba.
An ce, shugaban 'yan adawar kasar da ya yi kira da a kauracewa zaben, duk da cewa sunansa yana kan takardar zaben.
Kafofin watsa labarai na kasar sun bayyana cewa, domin zaben ya gudana yadda ya kamata, Kenya ta jibge 'yan sanda sama da dubu 13. (Lubabatu)