Masu sa idon dai sun bayyana zaben wanda bai samu yawan masu kada kuri'u ba, a matsayin wanda ya dace da tanaje tanajen kundin tsarin mulkin kasar Kenya.
Rahotanni sun bayyana cewa, rashin kyawun yanayi, da kuma tarzoma a wasu yankuna da ke da yawan 'yan adawa a kasar sun gurgunta zaben a wasu sassa.
Tsohon shugaban kasar Kenya Thabo Mbeki ne ya jagoranci tawagar AU don gani yadda zaben ya wakana, duk da cewa 'yan adawa sun kauracewa shiga a dama da su a zaben karo na biyu.
Da yake karin haske game da zaben, Mr. Mbeki, ya ce AU ta maida hankali ne katsokan ga tsarin gudanar zaben, ciki hadda hada sakamako daga runfunan zaben zuwa kirga alkaluman zaben. A hannu guda ya bayyana damuwa game da yadda jami'an zaben suka fuskanci tsangwama a wasu sassan da 'yan adawa ke da karfi.
AU dai ta tura jami'an sa ido zuwa gundumomi 20 na kasar Kenya. A ranar Litinin kuma hukumar zaben kasar ta ayyana shugaban kasar mai ci Uhuru Kenyatta, a matsayin wanda ya lashe zaben da aka kammala ranar 26 ga watan oktoba, da yawan kuri'u miliyan 7.48, kimanin kaso 98.26 bisa dari na jimillar wadanda suka cancanci kada kuri'u mutum miliyan 7.61. (Saminu)