Sakataren harkokin wajen kasar Amurka Rex Tillerson ya ce, ya yi farin ciki da hakurin da kasar Koriya ta Arewa ta yi bayan da kwamitin sulhu na MDD ya sanya mata wani sabon takunkumi, ya kuma nuna cewa, watakila za a samu damar yin tattaunawa a tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa.
Dangane da lamarin, madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana yau Laraba cewa, kasar Sin ta lura da bayanin da mista Tillerson ya yi, musamman ma jaddada batun yiwuwar yin tattaunawa a tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa. Madam Hua ta nuna cewa, sassa daban daban, musamman ma Koriya ta Arewa da Amurka za su ci gaba da kai zuciya nesa, tare da kara yin kokari. (Tasallah Yuan)