Bisa huldar dangantaka tare da kasar Sin ta fuskar soja, kasar Kenya na kara karfinta na fuskantar barazanar ta'addanci da kuma 'yan fashin teku, in ji wani babban jami'in kasar Kenya a ranar Alhamis a Nairobi.
Madam Raychelle Omamo, babbar jami'a dake ma'aikatar tsaron cikin gida ta bayyana cewa, dangantakar soja tsakanin Kenya da Sin ta kyautata tsaro da zaman karko a shiyyar kusurwar Afrika.
Sin da Kenya na ci gaba da karfafa dangantakarsu cikin armashi ta fannin tsaro domin baiwa kasashen biyu damar taka muhimmiyar rawa a cikin yakin da ake yi da ta'addanci a duniya, in ji madam Omamo a yayin wata liyafar da jakadan kasar Sin dake Kenya ya shirya a albarkacin bikin cikon shekaru 89 na rundunar sojojin 'yantar da kasar Sin (APL).
Madam Omamo ta nuna cewa, Kenya ta fifita dangantaka ta fuskar tsaro tare da kasar Sin bisa tsarin wata dubarar da ta shafi bunkasa zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyyar. (Maman Ada)