in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aikin jirgin kasan da Sin ke gudanarwa a Kenya zai bunkasa tattalin arzikin kasar
2016-08-09 10:43:00 cri
Wani ministan kasar Kenya ya bayyana aikin gina layin dogo da wani kamfanin kasar Sin ke gudanarwa da cewa, zai habaka cigaban tattalin arzikin Kenya da kuma saukaka harkokin sufuri ga al'ummar kasar.

Sakataren ma'aikatar samar da ababen more rayuwa da sufuri na kasar Kenya James Macharia, ya fada a lokacin taron karawa juna sani game da samar da ababen more rayuwa a Nairobi cewa, aikin wanda ya lashe kimanin dalar Amurka biliyan 3 da miliyan 600, an kammala kashi 88 bisa 100 na aikin, kuma tuni kasar ta samu karuwar kashi 2 cikin 100 na ma'aunin tattalin arziki na GDP a kasar.

Macharia ya ce, sama da 'yan kasar Kenya 27,000 ne suka samu ayyukan yi karkashin wannan aiki na shimfida layin dogo, kana al'ummomin dake makwabtaka da wajen da ake aikin, sun samu bunkasuwar harkokin kasuwancinsu.

Ya kara da cewa, aikin zai kara bunkasa tashar ruwa ta Mombasa, kasancewar za'a dinga gudanar da zirga-zirga jiragen ruwa cikin sauri a maimakon gudanar da sufuri ta titunan mota.

Bankin China's Exim ne ya samar da kudaden gudanar da aikin layin dogon mai nisan kilomita 472, wanda ya hada birnin Mombasa da Nairobi babban birnin kasar. Ana sa ran kammala aikin nan da shekara mai zuwa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China