Yayin bikin na jiya, jakada Liu Xianfa ya bayyana cewa, amfani da na'urorin da kasar Sin ta samar zai kara karfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da Kenya a fannonin hasashen yanayi da aikin gona da tinkarar sauyin yanayi da sauransu.
A nata bangare, Judi Wakhungu ta bayyana godiya ga kasar Sin bisa bayar da gudummawar, inda ta ce na'urorin da kasar Sin ta bayar kyauta sun bude wani sabon babi ga aikin hasashen yanayi a Kenya, kuma za'a girke su a sassa daban-daban na kasar, wadanda za su kunshi yankuna da dama.(Zainab)