Mr. Guo Ce ya yi wannan tsokaci ne cikin wani sharhi da wata jaridar kasar ta Kenya ta wallafa a Juma'ar nan, yana mai cewa kusan rabin daukancin ayyukan raya kasa guda 30, dake karkashin kudurorin kasar na samun ci gaba nan da shekarar 2030, sun samu ne sakamakon hadin gwiwar sassan biyu.
Mr. Guo ya kara da cewa, aikin layin dogo wanda kasar Sin ke daukar nauyin ginawa tsakanin biranen Mombasa zuwa Nairobi a kasar ta Kenya, shi ne aiki mai zaman kansa mafi girma da ake gudanarwa, a fannin ginin layin dogo a dukkanin gabashin Afirka.
Ya ce ya zuwa karshen shekarar bara, ginin layin dogon mai tsawon kilomita 480, ya samar da guraben ayyukan yi 42,000 ga al'ummar Kenya, ciki hadda kaso 42.3 bisa dari a fannin fasaha da na gudanarwa.
Mr. Guo ya kara da cewa, wannan layin dogo na zamani, zai baiwa Kenya damar zama a kan gaba wajen bunkasuwar sufurin jiragen kasa, wanda hakan zai mayar da ita cibiyar bunkasar tattalin arzikin ta fuskar masana'antu da cinikayya a yankin da take.(Saminu Alhassan)