in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Kenya sun daddale yarjejeniyar samar da gudummawar hatsi
2017-03-28 11:12:56 cri
A jiya 27 ga wata, aka daddale yarjejeniyar samar da gudummawar jin kai ta hatsi da gwamnatin kasar Sin za ta samarwa kasar Kenya, jakadan Sin dake kasar Kenya Liu Xianfa, da ministan harkokin kudi na kasar Kenya Henry Rotich sun daddale yarjejeniyar. Bisa yarjejeniyar, Sin za ta samar da gudummawar jin kai ta hatsi da nauyinsu ya kai fiye da ton dubu 20 don sassauta karancin hatsi a yanki mai fama da bala'in fari a kasar Kenya.

Bayan daddale yarjejeniyar, Liu Xianfa ya bayyana a gun taron manema labaru na hadin gwiwa da shi da minista Rotich suka gudanar tare cewa, Sin tana nuna kulawa sosai ga bala'in fari da kasar Kenya take fuskanta. Bisa bukatun gwamnatin kasar Kenya, gwamnatin kasar Sin ta samar da shinkafa da nauyinsu ya kai ton fiye da dubu 20 kaman darajarsu ta kai kudin Sin Yuan miliyan 150 ga kasar Kenya don taimakawa Kenya wajen tinkarar bala'in fari da rikicin yunwa a kasar. Ana sa ran cewa, za a kai gudummawar ne zuwa Mombasa na kasar Kenya, wadda za a ciyar da jama'a masu fama da bala'in kimanin miliyan 1 da dubu 400.

A nasa bangare, a madadin gwamnatin kasar Kenya da jama'arta, Rotich ya nuna godiya ga gwamnatin kasar Sin saboda samar da gudummawar jin kai ta hatsi ga kasarsa. Ya kara da cewa, yayin da kasarsa ta Kenya take fuskantar bala'in fari mai tsanani, gwamnatin kasar Sin da jama'arta sun samar da gudummawar jin kai ga jama'a masu fama da bala'in na kasar Kenya cikin gaggawa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China