Yau Litinin ne kasashen Amurka da Koriya ta Kudu suka fara atisayen soja na hadin gwiwa, da suka yi a ko wace shekara.
Dangane da lamarin, Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana a yau cewa, atisayen soja da Amurka da Koriya ta Kudu suke gudanarwa ba zai taimaka wajen sassauta halin da ake ciki a zirin Koriya ba, Sin ta bukaci sassa daban daban masu ruwa da tsaki da su kalli shawarar kasar Sin da idon basira, wato Koriya ta Arewa ta dakatar da shirinta na makamai masu linzami da na nukiliya, yayin da Amurka da Koriya ta Kudu kuma suka dakatar da atisayen sojan da suke yi. (Tasallah Yuan)