in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin Najeriya ya kama hanyar ci gaba, in ji Osinbajo
2017-10-11 20:28:26 cri

Mataimakin shugaban kasar Najeriya Yemi Osinbajo ya bayyana cewa, yanzu haka tattalin arzikin Najeriyar ya kama turbar ci gaba, bayan da ya fuskanci koma-baya tun a shekarar 2014.

Yemi Osinbajo wanda ya bayyana hakan yayin da ke kaddamar da taron kolin tattalin arzikin Najeriya karo na 23 da ya gudana jiya a Abuja, fadar mulkin kasar, ya ce sanin kowa ne cewa, tattalin arzikin Najetiya ya fuskanci koma-baya a rubu'i na biyu na wannan shekera, inda GDPn kasar ya kai kaso 0.55 cikin 100, yayin da hauhawan farashin kaya ya ci gaba da yin kasa daga yadda yake a can baya na kimanin kaso 18 cikin 100 a watan Janairun wannan shekara zuwa kimanin kaso 16 cikin 100 a wannan lokaci.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China