Gwamnan jihar Borno dake yankin arewa maso gabashin Najeriya Kashim Shettima, ya bayyana cewa, kimanin yara 52,311 ne suka zama marayu a jihar ta Borno sakamakon hare-haren kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar.
Gwamnan wanda ya bayyana hakan ga manema labarai jiya Alhamis a birnin Maiduguri, fadar mulkin jihar Borno, ya ce hare-haren kungiyar sun kuma raba mata 54,911 da mazajensu. A don haka ya ce muddin ba a yi wa tubkar hanci ba, lamarin na iya haddasa karuwar matsalar jin kai a jihar da ma yankin arewa maso gabashin kasar baki daya.
Ya ce, hukumomin jihar sun gano ilmi a matsayin hanyar magance wannan kalubale. Yana mai cewa, gwamnati ta himmatu wajen zuba jari a bangaren ilmi kana ta bullo da wasu shirye-shiryen agaji tare da hadin gwiwar gwamnatin tarayyar Najeriya, MDD da sauran abokan hulda na kasa da kasa. (Ibrahim)