in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ayodele Fayose ya bayyana burinsa na neman takarar shugabancin kasar Najeriya
2017-09-29 09:09:57 cri
Ayodele Fayose, gwamnan jahar Ekiti dake kudu maso yammacin Najeriya, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben shekarar 2019 karkashin jam'iyyar PDP wanda aka kwace mulki daga hannunta.

Shi dai Fayose dan jam'iyyar PDP ne.

Da yake jawabi a Abuja, fadar mulkin Najeriyar, gwamnan ya shedawa magoya bayansa cewa, shi kadai ne mutumin da zai iya yin galaba a kan shugaban kasar mai ci Muhammadu Buhari idan aka gudanar da sahihin zabe a kasar, sakamakon irin nasarar da ya samu a tarihin siyasarsa, wanda ya bayyana cewa tun da ya fara siyasa bai taba shan kaye a zabe ba.

Ya yi alkawarin cewar muddin aka zabe shi shugaban Najeriyar, zai gudanar da yaki da rashawa bisa adalci.

Ya kara da cewa batun tattalin arzikin kasar zai farfado da shi kuma zai samar da gagarumin ci gaba ga kasar fiye da gwamnati mai ci wanda ya bayyana a matsayin gwamnatin da ta gaza. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China