Da yake tabbatar da hakan a Juma'ar nan, mataimaki daraktan asusun na UNICEF Justin Forsythe, wanda ya gudanar da ziyarar aiki ta kwanaki 3 a yankin, ciki hadda birnin Maiduguri fadar mulkin jihar Borno, ya shaidawa manema labarai cewa, akwai yara kanana kusan miliyan daya da suka rasa matsugunnan su, ciki hadda yaran da shekarun su ba su wuce 5 ba, su kusan 450,000 da ake tsoron na iya rasa damar samun abinci mai gina jiki a yankin.
Kaza lika jami'in na UNICEF ya ce, bisa kiyasi akwai yara kanana miliyan 3 wadanda rikicin Boko Haram ya raba da makarantun su, a yankin na arewa maso gabashin Najeriya.(Saminu Alhassan)