in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wata cuta da ba a gano ta ba ta barke a jihar Bayelsa dake Najeriya
2017-10-05 12:08:19 cri

Rahotanni daga jihar Bayelsa mai arzikin mai a tarayyar Najeriya na cewa, an kwantar da mutane a kalla 11 a asibiti sakamakon wata cuta da har yanzu ba a gano ta ba.

Da yake tabbbatar da lamarin, kwamishinan lafiya na jihar Ebitimitula Etebu, ya ce cutar da ta karbe a jihar ta yi kama da cutar nan ta " Monkey Pox" wadda ke haddasa zazzabi, da zufa baya ga wasu kuraje dake fesowa wanda ke fama da ita.

Ya kuma shaidawa manema labarai cewa, an killace wani likita da wasu mutane 10 da ake ganin sun kamu da cutar a wata cibiya a jami'ar asibitin koyarwa ta Niger Delta dake Okolobiri, a karamar hukumar Yenagoa dake jihar ta Bayelsa.

Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya(NCDC) da tawagar masana a kan fatar jikin dan-Adam ta ma'aikatar lafiyar jihar ce suka kafa wannan cibiya, da nufin hada yaduwar wannan cuta.

Kwamishinan ya ce, yanzu haka an aika da samfurin kwayar cutar zuwa dakin binciken hukumar lafiya ta duniya dake Dakar na kasar Senegal domin tabbatar da hakikanin wannan cuta. Yana mai cewa, nauyin irin wannan cutar da ake samu a yammacin kasashen Afirka bai kai wannan hadari ba kuma babu wasu alkaluma dake nuna cewa, ya taba hakala wani mutum, haka kuma akwai kwayar cutar nauyin tsakiya da kuma yammacin kasashen Afirka.

Ya ce, alamomin cutar sun hada da tsananin ciwon kai, zazzabi, da ciwon baya da sauransu. Abin damuwa game da alamomin wannan cuta shi ne, manyan kurajen dake fitowa wanda ya kamu da cutar wadanda suka dara na cutar kyanda. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China