in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan bindiga sun yi garkuwa da jami'in dan sanda a arewacin Najeriya
2017-09-29 09:37:19 cri
Jiya Alhamis hukumar 'yan sandan Najeriya ta bada tabbacin cewa wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da Emmanuel Adeniyi, mataimakin kwamishinan 'yan sanda mai kula da sashen binciken masu laifuka a jihar Zamfara dake arewa maso yammacin kasar.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Zamfara Shaba Alkali, ya shedawa 'yan jaridu a Gusau, babban birnin jihar cewa, an yi garkuwa da Adeniyi ne a lokacin da yake kan hanyarsa ta Dandume/birnin Gwari a jihar Kaduna a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Gusau.

Alkali ya kara da cewa, an yi garkuwa da jami'in dan sandan ne a cikin jihar Kaduna, kuma har yanzu yana jiran cikakken bayani game da wannan al'amari.

A 'yan makonnin da suka gabata, wasu 'yan bindiga sun kaddamar da hari a kan ofishin 'yan sanda a Keta dake karamar hukumar Tsafe a jihar ta Zamfara, inda suka yi garkuwa da wasu jami'ai 3.

Batun garkuwa da mutane ba bakon abu ba ne a Najeriya. A 'yan kwanakin nan ana samun yawaitar yin garkuwa da baki 'yan kasashen waje da manyan mutane a kasar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China