Shugaban kasar Muhammadu Buhari, ya taya kungiyar murnar nasarar da ta samu a kan kungiyar Chipolopolo ta Zambia, yana mai bayyana nasarar a matsayin abu mai dadi da kwantar da hankali, kuma kyauta ta cikar kasar shekaru 57.
Wata sanarwar da ta shiga hannun kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ta ruwaito Shugaban kasar na yabawa kungiyar bisa kokarin da ta yi na sanya Nijeriya zama kasa ta farko a Afirka da ta yi nasarar samun cancantar shiga gasar cin kofin duniya ta 2018 da za a yi a Rasha.
Muhammadu Buhari ya kuma yi kira ga 'yan Nijeriya su rika zama masu juriya da hakuri da aiki tukuru da taimakawa juna a dukkan harkokinsu, wanda ya ce su suka kai 'yan wasan ga samun nasara tun bayan fara buga wasan neman cancantar.
Ya kuma lashi takobin gwamnatinsa za ta ci gaba da mara baya ga kungiyar da duk wani arziki da take da shi domin kasar ta fada kwarewarta a fannin wasannin musammam ma kwallon kafa. (Fa'iza Mustapha)