in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban jami'in MDD ya bukaci a maida hankali kan jama'a da duniya yayin da ake neman ci gaba mai dorewa
2017-10-04 13:13:20 cri
Mataimakin sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya, mai kula da harkokin tattalin arziki da zamantakewar al'umma, Mista Liu Zhenmin, ya bayyana cewa, ya kamata a kara mai da hankali kan jama'a da duniyarmu yayin da ake kokarin neman ci gaba mai dorewa. Liu ya kuma jaddada muhimmancin neman ci gaba daga dukkanin fannoni gami da bada tabbaci ga zaman rayuwar al'umma.

A yayin bikin kaddamar da kwamitin kula da harkokin zaman rayuwar al'umma, jin-kai da al'adu yayin babban taron MDD karo na 72, Mista Liu Zhenmin ya ce, neman ci gaba mai dorewa na bukatar yanayi mai kyau. Dukkan kasashe, walau kasashe maso tasowa, ko kasashe masu sukuni, ko manyan kasashe, ko kananan kasashe, suna fuskantar kalubale masu sarkakkiya yayin da suke raya tattalin arziki. Liu ya ce, a halin yanzu babban aikin dake gabanmu shi ne, taimakawa kasashen dake da matukar bukata.

Sabuwar kididdiga ta yi nuni da cewa, a halin yanzu, akwai mutane miliyan 766 wadanda ke zama cikin matsanancin talauci. Liu Zhenmin ya ce, idan aka ci gaba da bin tafarkin neman bunkasuwa na yanzu, sannan idan ba'a canja rashin nuna adalci a fannin albashi ba, kashi 35 bisa dari na mutanen dake zama a kasashe mafi fama da talauci, da kuma mutanen dake zama a kasashen dake fama da tashe-tashen hankula, za su ci gaba da zama cikin kangin talauci nan da shekara ta 2030.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China